Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 191 tare da kama 184

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa wacce aka fitar bayan wani taron manema labarai da rundunar ta yi a Abuja a ranar Alhamis, inda ta bayyana wasu nasarori da sojojin suka samu cikin mako guda.

Rundunar tsaron Nijeriya ta ce dakarun tsaron kasar sun kashe ‘yan ta’adda 191, sun kama 184 sannan sun kubutar da mutum 91 da aka yi garkuwa da su a wasu ayyukan samame da suka ƙaddamar a faɗin ƙasar.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da TRT Afrika ta samu, wacce aka fitar bayan wani taron manema labarai da rundunar ta yi a Abuja a ranar Alhamis, inda ta bayyana wasu nasarori da sojojin suka samu cikin mako guda.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Manjo Janar Edward Buba ta ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram 104 da su da iyalansu duk sun miƙa wuya ga sojoji, sannan an kuma kama mutum 22 da kitsa satar ɗanyen man fetur.

More News

Kotu ta sauke kakakin majalisar Nasarawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi dan jam’iyyar...

An sake gano gawar wani shugaban Fulani da ya ɓata a jihar Filato

An gano gawar wani Arɗon Fulani, Umar Ibrahim da ya ɓace a cikin wata rijiya dake kauyen Jokom a ƙaramar hukumar Mangu ta...

An kama ƴan kungiyar IPOB 18 da ake zargi da kisan ƴan sanda

Rundunar yan sandan jihar Imo ta kama mutane 18 da ake zargi da zama yan kungiyar IPOB da suke da hannu a kisan ƴan...

Masu cin gajiyar shirin Npower na kokawa game da rashin biyansu

Wasu masu cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na N-Power a ranar Litinin sun koka kan yadda ake ci gaba da biyan su alawus-alawus din...