Sojojin Nijar Sun Sako Salem Bazoum

Jami’an mulkin sojan Nijar sun sako Salem Bazoum ɗan gidan tsohon shugaban kasar Nijar, Muhamed Bazoum da sojojib suka yiwa juyin mulki kamar yadda wata sanarwa da kotun soja dake birnin Yamai ta fitar.

Salem mai shekaru 22 ya shafe watanni da dama a gidan shugaban kasa tare da mahaifansa tun lokacin da aka yi juyin mulki a cikin watan Yulin shekerar 2023.

Kotun sojan bata bada karin haske ba kan makomar iyayen Salem.

Wata majiya dake kusa da tsohon hanɓararren shugaban kasar ta faɗawa kafar yaɗa labarai ta AFP cewa Salem Bazoum ya bar birnin Yamai ya zuwa birnin Lome na kasar Togo.

Wata sanarwa da gwamnatin Togo ta fitar ta tabbatar da cewa an cimma matsaya domin sakin Salem bayan shiga tsakani da gwamnatin Togo da Kuma Sierra Leone suka yi.

Kasar Nijar na cikin takunkumi da kungiyar ECOWAS ta saka mata kuma ta bada sharadin sakin Bazoum tare da dawo da dawo da shi kan mulki a matsayin sharudan cire takunkumin.

More from this stream

Recomended