‘Sojojin Najeriya sun dauki alhakin kai hari Tudun Biri bisa kuskure’

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojojin Najeriya sun dauki alhakin jefa bam a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30 a ranar Lahadi.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an kashe mutane da dama a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna bayan da wani jirgin soji ya jefa bam a yayin da ake gudanar da bukukuwan Mauludi.

A kalla mazauna garin 30 ne suka mutu a lamarin wanda ya faru da misalin karfe tara na daren Lahadi.

Tun da farko dai rundunar sojin saman Najeriya ta musanta alhakin kai harin.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...