Sojoji sun sake kuɓutar da wata daga cikin ƴan matan Chibok

Sojojin bataliya ta 81 na rundunar Operation Hadin Kai sun ceto daya daga cikin yan matan Chibok da aka yi garkuwa da ita a shekarar 2014.

A cikin watan Afirilun shekarar 2014 ne mayakan kungiyar Boko Haram suka sace yan matan su 276 daga makarantar sakandaren yan matan dake Chibok.

Tuni aka ceto da yawa daga cikin yan matan.

Yarinyar da aka ceto mai suna Mary Nkeki an gano ta ne a ranar 25 ga watan Agusta a karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno.

Da yake magana a ranar Litinin a yayin mika ta ga gwamnatin jihar Borno, kwamandan rundunar, Gold Chibuisi ya ce an tilastawa Nkeki auren daya daga cikin yan kungiyar ta Boko Haram bayan da aka sace su tare da yan uwanta.

Da take magana kan halin da ta samu kanta a ciki a lokacin da take hannun yan ta’addar, Nkeki ta ce zama da yan ta’addar cike yake da wahala.

Nkeki ta ce ta tsere tare da mijinta da daddare daga sansanin yan ta’addar inda suka ci karo da sojojin dake sintiri.

Ta kara da cewa ta bar yan matan Chibok biyu a sansanin.

More News

An samu ambaliyar ruwa a Adamawa

Anguwan Tana, al’ummar karamar hukumar Yola ta Arewa, sun shiga tasgaro a ranar Alhamis sakamakon ambaliya daga kogin Kilange da kogin Faro. Mazaunan garin...

Sojoji sun ceto mutane 6 daga cikin ɗaliban jami’ar Gusau da aka sace

Sojoji sun ceto dalibai mata shida daga cikin daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau da aka bada rahoton yan bindiga sun yi garkuwa da...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

An sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba da sanyin safiyar Juma’a. ‘Yan ta’addan masu yawan gaske sun...

Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da...