Sojoji sun kashe yan bindiga da dama a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun samu nasarar kashe yan bindiga da dama a karamar hukumar Giwa dake jihar.

Samuel Aruwan kwamishinan tsaro na jihar shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce an kashe yan bindigar ne a wani farmaki da sojoji suka kai kan maboyarsu.

Sanarwar ta kara da cewa da yawa daga cikin yan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga ya zuwa yankin Hayin Siddi

More from this stream

Recomended