Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu mayaƙan Boko Haram biyar a wani farmaki da suka kai maboyarsu dake jihar Borno.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro kan yankin tafkin Chadi ya ce dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun kashe mayaƙan ne a farmakin da suka kai a dajin Sambisa.

Bayanai da ya wallafa ya ce sojojin da haɗin gwiwa dakarun soja na musamman sun kai farmakin ne a ranar Asabar a maɓoyar ƴan ta’addar dake ƙaramar hukumar Bama.

A cewar Makama majiyar jami’an sojan sirri ta bayyana cewa wasu daga cikin ƴan ta’addar sun tsere a yayin da aka kashe biyar daga cikinsu.

An samu nasarar kwato bindigogi uku ƙirar gida, bam guda biyu na bindigar  RPG, harsashi 23, gidan zuba harsashi 1 da kuma magunguna na daga cikin abin da aka samu a tare da ƴan ta’addar.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...