Sojoji sun kashe kwamandojin ƴan ta’adda a Najeriya

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ce bangarenta na rundunar Operation Hadin Kai a ranar 10 ga watan Janairu ya kawar da wasu manyan kwamandojin ISWAP da ‘yan ta’adda uku a Borno.

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaron, Maj.-Gen. Edward Baba, ne ya bayar da wannan tabbacin a cikin rahoton mako-mako na ayyukan rundunar a ranar Juma’a a Abuja.

Mista Buba ya ce kwamandojin uku an bayyana sunayensu kamar haka: Abou Maimuna, Abou Zahra da Kwamanda Saleh tare da kwamandansu a cikin kwalekwale.

Har yanzu dai jami’an tsaron Najeriya na ta fama ba dare ba rana wajen ganin sun kawar da ta’addanci a fadin ƙasar amma abin ya ci tura.

More from this stream

Recomended