Sojoji Sun Kashe Gawurtaccen Ɗan Bindiga Boderi

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu gawurtattun masu garkuwa da mutane da suka jima suna addabar al’umma.

Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Onyeama Nwachukwu shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis .

Ya ce ƴan fashin daji shida aka kashe a yayin farmakin da aka kai a yankin Bada-Riyawa dake kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar 22 ga watan Faburairu.

Ya ce bayanan sirri sun bayyana cewa Boderi da Bodejo  gawurtattun masu garkuwa da mutane na daga cikin yan fashin dajin da aka kashe a yayin arangamar.

Mutanen biyu sune ke da alhakin kai hari kan makarantar sojoji ta NDA,  kwalejin aikin gona dake Afaka, jami’ar Greenfield da kuma makarantar ƴan mata ta Yauri.

Baderi ya shafe shekaru da dama yana addabar al’umma kana ana zarginsa da haɗa baki da ƴan ta’adda domin kafa masu sansani a dazukan dake yankunan da yake da iko da su.

More from this stream

Recomended