Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga Biyu Tare Da Ceto Mutane 20 Da Aka Yi Garkuwa Dasu A Jihar Zamfara

Dakarun Rundunar Sojan Najeriya sun kashe ƴan fashin daji biyu ciki har da wani gawurtaccen ɗan bindiga a jihar Zamfara.

A wata sanarwa ranar Talata, Yahaya Ibrahim jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Hadarin Daji ya ce an kashe ƴan ta’addar ne a wani farmaki da aka kai maɓoyarsu dake kananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji a jihar Zamfara.

Ibrahim ya ce sojojin sun ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su da suka haɗa da mata da kuma ƙananan yara.

Ya ce sojojin sun samu nasarar lalata maɓoyar yan ta’addar da kuma maɓoyar wani fitaccen ɗan bindiga da ake kira Sule.

More from this stream

Recomended