Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram 18 A Dajin Sambisa

Jami’an rundunar sojan Najeriya ta Operation Hadin Kai sun kai farmaki kan wata maboyar yan Boko Haram dake surkukin dajin Sambisa a karamar hukumar Bama ta jihar Borno inda suka kashe mutane 18.

A cewar wakilin jaridar Daily Trust sojojin sun samu kwararan bayanan sirri kan sabon sansanin mayakan na Boko Haram inda suke haduwa tare da kitsa yadda za su kai hari yankunan Sheutari da kuma Mutari.

LWata majiya dake rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta na 21 Brigade Task Force dake Bama da hadin gwiwar jami’an Civilian JTF su ne suka kai farmaki maboya.

Shima wani masani kan yaƙin dake faruwa a yankin arewa maso gabas Zagazola Makama ya tabbatar da kai farmakin.

More from this stream

Recomended