Sojoji sun kashe ƴan bindiga 7 a Kaduna

Sojojin rundunar samar da tsaro ta Operation Safe Haven sun kashe yan bindiga 7 tare da gano makamai a ƙaramar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

A wata sanarwa ranar Talata mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Oya James ya ce sojojin dake gudanar da sintiri sun yi arba da yan bindigar ne a wurin da ake kira tudun Kachalla inda aka yi musayar wutar da ta kai ga kisan ƴan bindiga shida a yayin da wasu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Sanarwar ta ce an gano bindigar AK-47, harsashi masu yawa, waya kirar Tecno, babur da sauran abubuwa biyo bayan binciken wurin da aka yi artabun da sojoji suka yi.

Ya kara da cewa sojojin sun kuma kashe wani sanannen dan bindiga da ake kira da Musa Wada a ƙauyen Kondo dake ƙaramar hukumar.

Sanarwar ta cigaba da cewa mutane 33 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban aka kama a cikin makon da ya wuce.

More from this stream

Recomended