Sojoji sun kama wanda ake zargi ya kashe sabbin ma’aurata a Filato

Sojojin Najeriya karkashin Operation Safe Haven, OPSH, ta cafke wani da ake zargin ya kashe wasu ma’aurata a kauyen Kwi da ke karamar hukumar Riyom a jihar Filato.

Lt.-Kol. Ishaku Takwa, Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Runduna ta 3 ta Sojojin Najeriya, Rukuba, kusa da Jos, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Asabar a Jos.

Idan ba a manta ba a ranar 14 ga watan Agusta, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wasu sabbin ma’aurata, daya mai suna Rwang Danladi mai shekaru 37 da matarsa, Sandra mai shekaru 28.

Ma’auratan, dukkansu malaman sakandaren BECO Comprehensive Secondary School, da ke Kwi, an kashe su ne a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a makarantar.

Mista Takwa ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 18 ga watan Nuwamba a unguwar Tafawa da ke Barkin Ladi, biyo bayan jajircewar da sojojin suka yi.

More from this stream

Recomended