Sojoji sun kama masu wadatar makamai a jihar Taraba

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kama wasu mutane biyu da ke safarar bindiga inda suka gano makamai da kuma harsashi a tare da su a jihar Taraba.

An samu nasarar damke mutanen ne biyo bayan wani samame da dakarun sojan su ka kai da ya samu daukin sashen leken asiri da tattara bayanan sirri na ma’aikatar tsaro ta Æ™asa.A

Wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, Umar Muhammad mai rikon mukamin daraktan hulÉ—a da jama’a na rundunar sojan  ya ce an kama Christopher Adamu da James Yangyang a Sebos Joint dake yankin Mayo Dassa a Jalingo da kuma kauyen Tutre dake karamar hukumar Ardo-Kola.

Muhammad ya ce an kama mutanen ne sakamakon sanya idanu da kuma kai kuma samame na tsanaki da dakarun rundunar suke yi domin ruguza shirin batagari na watsa Æ™ananan makamai a cikin al’umma.

Ya kara da cewa rundunar ta kuma ayyana gano bindigar kirar AK-47 a gidan Bazoe John dake kauyen Murubai a karamar hukumar ta Ardo Kola duk da cewa zakara ya bashi sa’a ya tsere.

More from this stream

Recomended