Sojoji sun hallaka ƴan ta’adda 14 a Arewa maso Yamma, sun kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su

Dakarun runduna ta 1 ta sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 14 tare da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a wani samame na baya-bayan nan a jihohin Neja da Kaduna, kamar yadda rundunar ta sanar a ranar Lahadi.

A wata sanarwa a dandalin X, mai magana da yawun rundunar Laftanar Kanar Musa Yahaya ya ce sojojin sun fatattaki ‘yan ta’addan daga maboyarsu, inda suka yi nasarar kwato muggan makamai tare da kubutar da wadanda suka yi garkuwa da su.

“A ranar Asabar a Jihar Neja, sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyen Madawaki, inda suka kashe biyu tare da tilasta wa wasu tserewa. Sun kwato bindigogi kirar AK-47, alburusai, da babur.

“A sansanin da aka kashe jagoran ‘yan ta’addar Ali Kachalla, sojoji sun ceto maza 13 da aka yi garkuwa da su a watan Oktoba. Sun kuma gano fasfo mai alaka da wata babbar kungiyar ta’addanci.

“Bincike a sansanin ya kai ga ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su, dukkansu maza. An bayyana cewa an sace mutanen ne a jihar Neja a ranar 13 ga Oktoba, 2023.

“Abubuwan da aka kwato daga sansanin sun hada da fasfo na kasa da kasa da ake zargin na da wata babbar alaka ne da masu tayar da kayar baya,” in ji sanarwar.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...