Sojoji sun hallaka ƴan bindiga a Zamfara

Dakarun Operation Hadarin Daji sun ceto mutane 24 da aka yi garkuwa da su tare da kawar da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya sanya wa hannu inda ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da dakarun bataliya ta 223 da ke aiki a karkashin sashe na 1 na rundunar hadin gwiwa ta Operation Arewa maso Yamma Hadarin Daji suka kai dauki.

Ya ce sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, inda suka kashe 4 daga cikinsu tare da kubutar da 24 daga cikin wadanda aka sace.

“Rundunar sojojin da ke karkashin kwamandan Bataliya, sun yi wa ‘yan bindigar dirar mikiya, inda suka halaka 4 daga cikinsu a wani kazamin fadan wuta da ya barke.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...