Jami’an rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar dakile wani hari da mayakan kungiyar ISWAP suka yi kokarin kai wa a karamar hukumar Monguno ta jihar Borno.
Zagazola Makama masani dake wallafa rubutu kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce sojojin shiya ta 3 na rundunar kasa da kasa wato MNJTF su ne su ka yi artabu da yan ta’addar.
Makama ya ce yan ta’addar sun farma yankin a cikin motocin Hilux da dama da aka girkawa bindigar harbo jirgi a saman su a ranar Alhamis.
Bayanan da ya wallafa sun bayyana cewa wasu daga cikin yan ta’addar sun zo akan babura a yayin da wadanda su ke a kafa suka farma sojojin dake Charlie 6 a cikin garin Monguno.
A karshe dai yan ta’addar sun tsere.