‘Yan bindiga a maboyarsu da ke kewayen Kagarko, Iche, Taka-Lafiya Gidan Makeri da Jangala a Jihar Kaduna an ce sun tsere bayan da sojoji sama da 100 suka mamaye dajin karamar hukumar Kagarko.
Al’ummomi da dama a masarautar Kagarko sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da suka yi awon gaba da mazauna yankin da manoma, lamarin da ya sa jama’a suka kasa jurewa.
Bayan isowar sojojin da suka kai farmaki maboyarsu da wasu al’ummomin karkara tare da kame wasu da ake zargin masu ba da labari, an shawo kan lamarin, kuma an samu zaman lafiya a yankin.
Wani mai rike da sarautar gargajiya a garin Kagarko, Suleiman Aliyu, ya ce sojojin da suka shiga garin Kagarko da misalin karfe 11 na safiyar ranar Laraba a cikin motocin Hilux da manyan motoci da babura, sun zarce zuwa kauyukan Iche, Taka-Lafiya, Gidan Makeri da Janjala da ke kusa da dajin, don farautar ‘yan fashi.