Sojoji sun ceto wasu mata da aka yi garkuwa da su a Kaduna

0

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kakkabe wata maboyar yan bindiga tare da ceto Wasu mata da aka yi garkuwa da su a Chikun dake jihar Kaduna.

Biyo bayan nasarar da suka samu a karshen mako ta kashe yan bindiga masu yawan gaske jami’an tsaron sun cigaba da aikin raba dazukan jihar da yan bindiga.

Bayanan da gwamnatin ta Kaduna ta samu sun bayyana cewa rundunar Operation Forest Sanity ta kai farmaki tare da aikin ceto a ƙauyukan Kuriga da Manini a karamar hukumar Chikun.

Matan da aka ceto sun hada da

_ Sahura Hamisu
– Ramlatu Umar
– Saudatu Ibrahim
– Maryam Shittu
– Fatima Shuaibu
– Khadijah Mohammed tare da danta.