
Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta da suka fito daga birged ta 12 sun ceto wasu mutane 6 daga hannun masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Yagba East dake jihar Kogi.
A wata sanarwa ranar Talata, Hassan Abdullahi mai magana da yawun birged ta 12 ya ace an ceto mutanen ne a dazukan Ejiba da Saminaka dake jihar ta Kogi.
Abdullahi ya ce farmaki hadin gwiwa ta sama da ƙasa da taimakon jirgin yan sanda mai saukar ungulu ne ya kai ga kubutar da mutanen bayan da masu garkuwa da su suka tsere suka barsu sakamakon matsin lamba daga dakarun sojan.
Ya ce farmakin wani ɓangare ne na kokarin da ake wajen shawo kan garkuwa da mutane da ke cigaba da yin ƙamari a fadin jihar.
” Biyar daga cikin mutanen da aka ceto an mika su ga iyalansu a garin Egbe da Ejiba a yayin da mutum na shida ke samun kulawar likitoci,” a cewar sanarwar.

