
Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun samun nasarar ceto wasu mutane 24 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Sojojin sun samu nasarar ceto mutanen ne biyo bayan bayanan sirri da suka samu kan wata maboyar yan bindiga dake dajin Kabugu Lamba.
A cewar rahotanni sojojin sun yi musayar wuta da yan bindigar abin da ya tilasta musu tserewa da kafafunsu tare da barin wadanda suke garkuwar da su.
Yan bindiga hudu ne suka mutu a yayin arangama da sojojin yayin da sauran suka gudu da raunin harbin bindiga
Mutanen da aka kubutar sun haɗa da maza 14 jariri 1 da kuma mata 9 da tuni aka miƙa su ga hukumomin da ya dace domin haɗa su da iyalinsu.