Sojoji Sun Ceto Mutane 16 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

Rundunar Sojan Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 16 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su daga ƙauyen Tantatu a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A ranar Lahadi ne ƴan fashin daji su ka farma garin na Tantatu da misalin ƙarfe 10 na dare inda suka farfasa shaguna suka sace kayan abinci da kuma sauran kayayyaki a gidajen jama’a.

Aƙalla mutanen garin 87 aka ce maharan sun ɗauke a yayin farmakin.

Ko da a ranar Asabar ma mutane 14 aka bada rahoton an sace a ƙauyen Dogon Nama dake ƙaramar hukumar ta Kajuru.

A wata sanarwa ranar Litinin, Onyeama Nwachukwu mai magana da yawun Rundunar Sojan Najeriya ya ce sojojin sun amsa kiran da aka yi musu bayan da aka kai hari garin ranar Lahadi da da daddare.

Nwachukwu ya ce sojojin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar har ta kai ga an samu nasarar ceto mutanen.

Ya ƙara da cewa sojojin na cigaba da bincike cikin dajin a ƙoƙarin ceto ƙarin wasu mutanen.

More from this stream

Recomended