


Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun kashe akalla mutane 10 da ake zargin yan bindiga ne a jihar Zamfara.
A cewar Zagazola Makama wanda yake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce an kashe yan bindigar ne a wani harin kwanton ɓauna da sojoji suka maisu a yankin Gadan Zaima zuwa Dan Marke dake karamar hukumar Bukuyyum a ranar Talata.
Wasu majiyar sojoji ta bayyana cewa biyo bayan musayar wuta sojojin sun kuma samu nasarar kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a wani daji dake iyakar Mahuta da Zuru a jihar Kebbi.
Majiyar ta ce yayin da aka samu nasarar kashe wasu daga cikin an kuma samu nasarar kama wasu.
Makama ya kara da cewa bingogi shida kirar AK-47, bindigar GPMG kudi naira miliyan 1 da kuma tabar wiwi aka gano a wurin yan bindigar.