
Sojojin bataliya ta 112 a rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar kashe ƴan ta’adda uku a lokacin da suke ƙoƙarin kai wa manoma hari a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun yi wa mayaƙan kwanton ɓauna inda suka kashe uku wajejen yankin Manawaji a ranar 07 ga watan Nuwamba.
Sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutane bakwai da yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Har ila yau sojojin sun samu nasarar kwace bindiga kirar AK-47 ɗaya da baburan hawa biyu daga hannun yan bindigar.