
Rundunar sojan saman Najeriya Najeriya ta lalata wata haramtacciyar matatar dake kauyen Dariama a jihar Rivers.
Sashen sojan sama na rundunar Operation Delta Safe ta samar da zaman lafiya a yankin Niger Delta shi ne ya kai hari kan matatar.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayan kan sha’anin tsaro an kai harin ne biyo bayanan sirri da aka samu kan haramtacciyar matatar dake kauyen na Dariama dake da tazarar kilomita 20 kudu maso yammacin Abonnema.
Wata majiya dake jami’an tsaro ta fadawa Makama cewa matatar na da ramuka da kuma tan kuna dake cike da fetur.