Shugabar Jamus tana zawarcin Najeriya, da yammacin Afrika

[ad_1]

Hakkin mallakar hoto
AFP

A daidai lokacin da Firayim ministar Birtaniya, Theresa May, take ziyara a Najeriya a cigaba da ziyararta a nahiyar Afrika, wata takwararta daga Turai ita ma tana nahiyar ta Afrika.

Shugabar Jamus, Angela Merkel, tana ziyara a Senegal, kuma za ta ziyarci Ghana da Najeriya.

Shin me ya sa take ziyara? Dalilin ziyararta dai daya yake da na Misis May – bunkasa cinikayya da nahiyar Afrika.

A wani jawabin bidiyo da ta yi kwanan nan Misis Markel ta ce: “Kasashen Afrika ka iya kasancewa kyakkyawar kasuwa nan gaba.”

Ta kara da cewa: “Sauran kasashe sun riga sun fara haraka da haniyar.”

Da alama kowa na kokarin zawarcin Afrika , wurin da China da Faransa da kuma Amurka suka dade suna taka muhimmiyar rawa.

Yawan al’ummar da ake da su a Afirka da kuma bukatar kayayyakin amfanin yau da kullum da ake kerawa a kasashen da suka ci gaba na daga abubuwan da suka sa kasashen suke rububin Afirka.

Kasashen da suka ci gaba suna so su ci moriyar babbar kasuwar da ake da ita a Afirka da kuma damammakin kasuwanci da cinikayya.

To sai dai wasu masu sharhi na ganin ya kamata su ma kasashen na Afirka su yi amfani da wannan damar wajen gabatar da bukatun su ga manyan kasashen da suka ci gaba.

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...