Shugaban Tchadi Idris Deby ya zama Marshal

Janar Idris Deby

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai majalisar dokokin kasar ta Tchadi ta amince da wata doka da ta kara wa shugaban kasar Idrissa Deby Itno girma daga Janar zuwa mukamin Marshal – wanda shi ne mukamin da ya fi kowanne a tsarin aikin soji.

Wannan Karin mukami ya biyo bayan gwagwarmayar da ‘yan kasar suke ganin shugaban ya jagoranta zuwa filin daga domin yin artabu da mayaka masu ikirarin Jihadi a kasar tare da tura sojojinsa zuwa Mali da Najeriya .

Irin wannan mukami ne dai marigayi Idi Ameen na Uganda da Mabutu sese seko na Zaire da kuma Jean Bedel Bokassa na jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka rike.

Masu fashin bakin siyasa na yi wa wannan mukami kallon wani yunkuri na tabbatar da kai a karagar mulki.

Idris Deby Itino na son wanzuwa kan mulki

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Idris Deby ne shugaban Tarayyar Afirka daga 2016 zuwa 2017

Farfesa Addo Mahamane wani masanin siyasa da tarihi kuma shugaban jami’ar jihar Tawa a jumhuriyar Nijar ya shaida wa BBC cewa “wannan ba wani abu ba ne illa yunkurin shugaban na Tchadi da neman tabbatar da kai a matsayin shugaban kasar na har abada.”

Farfesa Mahamane ya kara da cewa “matasayin na Marshal da aka ba shi ya nuna irin yadda majalisar ta ke yi wa Idris Deby kallon shi jarumi ne dangane da jagorantar dakaru a filin yaki sannan zai samar da tsaro a kasashe da dama kenan shi ne zai iya samar da mafita.”

“Wannan na cikin wani irin rudi da shugabannin Afirka ke sa kansu a ciki na yi wa kansu kallon su daban suke da sauran al’umma saboda haka su ne ma ya kamata su dawwama suna mulkin jama’ar tasu. Mun ga dai yadda Idi Ameen da Mabutu sese seko da kuma Jean Bedel Bokassa suka yi,” in ji farfesa Mahamane.

Masanin siyasar ya kara da cewa bai wa shugabanni kasashe mukamin Marshal ba wani abu zai haifar ba ga kasashen Afirka illa kokarin sanya wa al’ummar kaunar mulkin soji kasancewar ana nuna shugabannin su ne jaruman da za su iya samar da zaman lafiya ga al’umma.

“Kenan wannan babban hadari ne ga mulkin dimokradiyya a nahiyar Afirka,” kamar yadda farfesa Mahamane ya shaida.

Wane ne Idris Deby?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Janar Idriss Deby mai ritaya ya karbi mulkin kasar Chadi ne a shekarar 1990 bayan ya jagoranci tawayen da ya kawo karshen mulkin Shugaba Hissene Habre.

An yi zaben raba-gardama wanda ya kawo sauyi ga tsarin mulkin kasar, wanda ya bai wa Shugaba Deby damar tsaya wa takara ya kuma yi nasara a watan Yunin 1996.

Shugaba Deby ya kara lashe zabe a shekarar 2001.

A 2005 ne kasar ta tsunduma cikin yakin basasa tsakanin Musulmi da Kirista.

An yi zaben raba-gardama a watan Yunin 2005 wanda ya soke dokar wa’adi biyu ga shugaban kasar, kuma ya bai wa Deby damar sake tsayawa takara.

A 2006 ne aka yi yunkurin yi masa juyin mulki ta hanyar harbo jirginsa a shekarar 2006, amma hakan bai yi nasara ba.

A ranar 8 ga watan Agusta ne kuma aka kara rantsar da Deby a matsayin shugaban kasar a shekarar 2006.

An sake rantsar da shi a wa’adi na hudu a watan Afrilun shekarar 2011, bayan ya samu gagarumin rinjaye a babban zaben kasar.

Kuma a farkon wannan shekarar aka sake yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul tare da maido da tsarin wa’adi biyu ga shugaban kasa.

Yayin da kuma ya yi ratsuwar ci gaba da mulki a karo na biyar a ranar 8 ga watan Agustan 2016.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...