Shugaban sojojin Saudiya ya kai ziyara Iran

Babban hafsan sojojin ƙasar Saudiyya ya kai ziyara Tehran babban birnin kasar Iran domin tattaunawa da takwaransa na ƙasar Iran da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnatin ƙasar.

Irin wannan ziyara ta manyan jami’an tsaron kasashen biyu ba a saba ganin irinta ba tun bayan da ƙasashen biyu suka sake ƙulla alaƙa a shekarar da ta wuce.

Fayyad al-Ruwaili babban hafsan sojan ƙasar Saudiya ya gana da takwaransa na Iran  Janaral Muhammad Bagheri  a hedkwatar sojojin kasar Iran a ranar Lahadi.

A cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasar Iran IRNA  tattaunawar tasu ta mayar da hankali kan bunƙasa diflomasiya kan sha’anin tsaro da kuma faɗada yarjejeniyar haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen.

Bagheri ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin kai ta fannin tsaro a tsakanin ƙasashen biyu a wurin taron.

More from this stream

Recomended