Shugaban sojin saman Nigeriya ya gana da wadanda harin jirgin sama ya rutsa da su a Nasarawa

Shugaban Rundunar Sojan Sama Air Marshal Hasan Abubakar, ya gana da iyalai da wadanda harin bazata ya rutsa da su a ranar 24 ga Janairu, 2023, kusa da Rukubi a karamar hukumar Doma ta Jihar Nasarawa.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin saman Najeriya NAF, AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.

A taron da aka yi a Lafiya a ranar 26 ga watan Janairu, hukumar sojin ta nuna nadamar faruwar lamarin, inda ta ce rahotannin da suka shigo sun nuna cewa akwai yiwuwar an kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba bisa kuskure a yayin gudanar da aikin.

More News

Ƴanbanga sun sake kawar da wani ƙasurgumin ɗanbindiga

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa an yi nasarar kawar da wani fitaccen dan bindiga a jihar Zamfara,...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Majalisar dokokin Zamfara ta tsige kakakinta saboda tsanantar rashin tsaro a jihar

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, tare da nada Bashar Gummi, a matsayin kakakin majalisar. Hakan ya biyo bayan kudirin da dan...

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane shida da wasu ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari a jihar. Jami’in hulda...