Shugaban Liberia ya rage albashinsa

Shugaban Liberia Joseph Boakai ya sanar da yanke kaso 40 na albashinsa, kamar yadda ofishinsa ya sanar.

Shugaban ya ce ya ɗauki matakin ne domin zama wani dalili na yunƙurin tabbatar da shugabanci nagari da kuma tausayawa al’ummar Liberia.

Wannan na zuwa yayin da ƴan Liberia ke ƙorafi kan tsadar rayuwa a kasar.

Alƙalumma sun nuna mutum ɗaya cikin biyar na rayuwa ne ƙasa da dala biyu a Liberia.

A watan Fabrairu, Mista Boakai ya sanar dacewa dala 13,400 ne albashinsa na shekara. Yanzu kuma albashin zai dawo dala 8,000 bayan yanke kaso 40.

A baya dai, tsohon shubaban kasa George Weah,ya yanke kaso 25 na albashinsa.

Mutane da dama daga yammacin Afirka sun jinjina wa shugaban, amma wasu na ganin wannan sadaukarwar ba wani abin a yaba ba ne domin akwai wasu kuɗaɗe na alawus da kuma kula da lafiyarsa da shugaban yake karɓa.

A bana kasafin kudin ofishin shugaban ƙasar Liberia ya kai dala miliyan uku

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...