Shugaban jam’iyyar APC na jihar Oyo ya mutu

Shugaban jam’iyar APC na jihar Oyo, Isaac Omodewu  ya mutu.

Omodewu ya mutu ne a ƙasar Amurika inda yaje ganin likita.

A cikin watan Nuwamban shekarar 2023 ya bar Najeriya domin ganin likita.

Amma kuma ya mutu bayan da ya shafe kusan shekara guda yana jinyar wata cuta da ba a bayyana ba a ƙasar ta Amurka inda yake da shedar zama ɗan ƙasa.

Olawale Sadare mai magana da yawun jam’iyar a jihar Oyo shi ne ya tabbatar da haka a ranar Litinin.

” Shugaban mu ya mutu,” ya ce.

Marigayin ya taɓa riƙe muƙamin kwamishina a gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abiola Ajimobi.

More from this stream

Recomended