Shugaban DSS ya ajiye aikinsa

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Yusuf Magaji Bichi ya shirya miƙawa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu takardarsa ta yin murabus a ranar Litinin.

Wasu majiyoyi dake hukumar ta DSS sun bayyana cewa daraktan ya faɗawa na kusa da shi da maraicen rana shirinsa na yin murabus.

Shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ne ya naɗa shi shugabancin hukumar a shekarar 2018 domin ya maye gurbin Matthew Seiyefa wanda ya yi shugabancin hukumar na riƙo.

A ranar Asabar ne takwaran aikinsa na Hukumar Leƙen Asiri ta Najeriya NIA, Ahmed Rufa’i ya miƙa takardarsa ta barin aiki ga shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu.

More from this stream

Recomended