Shugaban Burundi ya nemi a fara jefe ƴan luwaɗi a ƙasar

Shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye, ya nuna ƙyamarsa ga ‘yan luwadi a ranar Juma’a, yana mai cewa ya kamata a riƙa jefe ma’auratan jinsi daya a bainar jama’a.

Har ila yau ya caccaki kasashen yammacin duniya da ke matsa wa wasu kasashe su ba dama wa ‘yan luwadi ko kuma su rasa taimako.

Luwaɗi a Burundi, watau kasar Kirista masu ra’ayin mazan jiya a gabashin Afirka, laifi me da tun shekara ta 2009 aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.

More from this stream

Recomended