A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a karkashin inuwar jam’iyyar Progressive Governors Forum (PGF).
Shugaban PGF, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya jagoranci wasu takwarorinsa goma sha hudu zuwa taron.
Sauran gwamnonin sun hada da na Kwara, Benue, Kaduna, Ekiti, Cross River, Ogun, Borno, Yobe, Kebbi, Jigawa, Ondo, Kogi, da Sokoto, sun halarci taron.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda kotun koli ta tabbatar da nasarar zabensa a yau, bai halarci taron ba.
Taron yana gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar shugaban kasa.
Ba a san ajanda taron ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.