Shugaba Tinubu ya jajanta kan rasuwar Sarkin Ningi

Shugaba Bola Tinubu ya jajanta wa al’ummar Masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi bisa rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.

Allah ya yi wa sarkin mai daraja ta daya rasuwa ne da sanyin safiyar Lahadi.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin hazikin shugaba wanda ya yi amfani da mulki da dukiyar sarautarsa wajen yi wa al’ummarsa hidima.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma yi ta’aziyya ga iyalansa da duk wadanda ke cikin alhinin rashin.

More from this stream

Recomended