Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce Shugaban kasa Bola Tinubu ba ya daukar lamarin kalubalen tsaron kasar da wasa.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake karbar shugabannin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a fadar shugaban kasa.
“Halin tsaro a kasar wani abu ne da shugaban kasa ke matukar sha’awar shi kuma baya daukarsa da wasa,” in ji mataimakin shugaban kasar a wata sanarwa da kakakinsa Stanley Nkwocha ya fitar.
“Laccar kasa da kasa da NAN ke shiryawa ya dace sosai, musamman kan batun rashin tsaro a yankin Sahel.”
Ya yi kira da a yi kokari na shiyya-shiyya da na gamayya don magance matsalar rashin tsaro a yankin Sahel na yammacin Afirka, duba da yadda yanayin tsaro a yankin Sahel ke da matukar tasiri ga Najeriya da kuma kasashen da ke makwabtaka da ita.