Shin Yaushe Za’a Bude Sufurin Jiragen Kasa-da-Kasa a Najeriya?

Hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya NCAA, ta bayyana cewa za ta kara wa’adin bude sashen tashi da saukan jirage na kasa-da-ka a filayen jiragen sama har zuwa 19 ga watan Oktoba, a maimokon 19 ga watan Augustar da ta bayyana a baya.

Adamu Abdullahi, darakta a hukumar ta NCAA ne ya bayyana wannan matakin a wata hirar da yayi da jaridar BusinessDay.

Abdullahi ya ce ba za’a fara zirga-zirgar jiragen sama na kasa-da-kasa ba har sai nan da watan Oktoba.

“Idan mun sauya matsayarmu, za mu bayyana sabon hukuncin da mu ka dauka,” in ji Abdullahi.

Hakan na nufin cewa jirage masu aiki na musamman da na jami’an difilomasiyya ne kadai aka baiwa dama a halin yanzu, har sai an tabbatar da lokacin bude zirga-zirgar kasa-da-kasa.

A cikin watan Maris din da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa-da-kasa domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

More from this stream

Recomended