Shin yaushe za a kawo ƙarshen zanga-zangar EndSars?

masu zana-zangar endsars

Zanga-zangar adawa da rundunar yaƙi da fashi da makami da ake kira SARS na ci gaba da bazuwa a sassan Najeriya, inda yanzu ta shiga mako na uku.

An soma zanga-zangar ne kan zargin da wasu ƴan Najeriya ke yi wa rundunar SARS na azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da kuma saɓa ƙa’idojin aiki.

Amma kuma zanga-zangar ta haifar da wata zanga-zangar musamman a jihohin arewaci ta neman kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Zanga-zangar ta tilasta wa gwamnati rusa rundunar ta SARS, amma matakin sai ƙara rura wutar zanga-zangar ya yi, al’amarin da wasu ke ganin na neman rikiɗewa ya koma rikici, inda suke ganin ana son karkatar da zanga-zangar daga asalinta.

Akwai wasu buƙatu da masu zanga-zangar ke son a biya masu bayan da gwamnati ta rusa rundunar ta SARS da nufin lallashin ƴan Najeriya kan fusatar da suka yi.

A cikin jawabin da ya yi wa ƴan Najeriya a makon da ya gabata bayan rusa rundunar, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ta damu da ƙorafin ƴan Najeriya kan amfani da ƙarfi sama da ƙima da ƴan sanda ke yi da kuma kisa mara dalili.

Shugaban ya ce soke rundunar, matakin farko ne a sauye-sauye masu tsauri da zai aiwatar kan aikin ƴan sanda domin tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi aikin da ya dace da kare rayuka da dukiyoyi.

Amma masu zanga-zangar sun yi biris da a

lƙawalin da shugaban ya yi na tabbatar sauye-sauye a aikin ɗan sanda a Najeriya.

Buƙatun masu zanga-zangar EndSars

Gwamnati da wasu shugabannin ‘yan kasuwa sun yi kokarin shawo kan matasa su kawo ƙarshen zanga-zangar da suke saman tituna amma masu zanga-zangar sun dage kan wasu buƙatu guda biyar da suke son gwamnati ta aiwatar, idan ba haka ba za su ci gaba da zanga-zangar.

Buƙatun sune kamar haka:

  • A saki dukkanin masu zanga-zangar da aka kama
  • A gurfanar da dukkanin ‘yan sandan da suka ci zalin ‘yan Najeriya sannan a biya iyalansu diyya
  • A kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai sa ido kan binciken cin zarafi da ‘yan sanda suka aikata da kuma hukunta su cikin kwana 10
  • A yi wa dukkanin dakarun rundunar SARS gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa kafin sauya musu wurin aiki
  • A ƙara wa ‘yan sanda albashi.

Bayan rusa rundunar SARS, gwamnati ta ƙirƙiri wata runduna ta musamman da ta kira SWAT wacce ta ce za ta ci gaba da aikin rundunar SARS.

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce kafin ɗaukar jami’an da za su yi aiki a sabuwar rundunar SWAT sai an yi gwajin lafiyar ƙwaƙwalwasu domin tabbatar da dacewarsu ta gudanar da aikin rundunar tare da ba su horo na musamman.

Gwamnatin Tarayya kuma ta ce za ta kafa kwamitocin bincike a kowacce jiha da za su zaƙulo waɗanda ‘yan sanda suka ci zarafinsu domin yi musu adalci.

A makon da ya gabata mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce jihohi za su kafa kwamitocin shari’a domin binciken cin zarafi da ‘yan sanda suka aikata.

A nasu ɓangaren majalisun dokokin tarayya sun ce sun ƙaddamar da kwamitocin da za su yi nazari ga kundin tsarin mulki kan sake fasalin rundunar ƴan sanda.

An yi gaggawar kafa SWAT

Masu zanga-zangar sun nuna rashin goyon bayansu kan sabuwar rundunar SWAT da aka kafa da nufin maye gurbin SARS, inda suke cewa hakan tamkar an koma gidan jiya ne.

Masana kamar Group Captain Saddik Shehu mai ritaya mai sharhi kan al’amuran tsaro a Najeriya, na ganin an yi gaggawar kafa rundunar yayin da wasu ke zanga-zanga.

“Ni a gani na shugaban ‘yan sandan Najeriya ya yi azarɓaɓi wajen kafa wannan SWAT ɗin,” In ji shi.

Ya ce ce-ce ku-ce ne kawai ya yi wa shugaban ‘yan sandan yawa da matsin lamba ya sa ya kafa wannan rundunar cikin gaggawa.

A cewarsa “tun da gwamnati ta rushe SARS, sai a tsaya a yi tunani kafin a san abin da za a fito da shi, amma a ce an rushe SARS jiya, yau da safe a ce an tashi an koma SWAT, kafa SWAT ba ƙaramin aiki ba ne.”

Gwamnati na yin kaffa-kaffa

Bayanan hoto,
Zanga-zangar ta haifar da cunkosun ababen hawa a Abuja

Zanga-zangar EndSars ta ja hankalin duniya, musamman ma fitattun mutane irin su ‘yan kwallon ƙafa da mawaƙa, da taurarin fina-finai.

Tsawon mako biyu masu zanga-zangar na fitowa saman titi musamman a Abuja da Legas ba fashi, duk da gwamnati ta ɗauki mataki tare da alƙawalin biyan buƙatunsu.

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban Jam’iyyar APC na riko, Alhaji Mai Mala Buni, ya ce “ci gaba da zanga-zangar, alama ce da ke nuna cewa akwai masu ɓoyayyar manufa bayan gwamnati ta saurari kukan matasan – kuma ya kamata a yi kaffa-kaffa da su.”

A hirarsa da BBC Gwamna Buni ya yi zargin cewa akwai ɓata gari, wadanda a ganinsa su ne wannan rundunar ta EndSARS ke ƙoƙarin kawarwa.

Ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakan mulki da su “dawo cikin hayyacinsu” saboda sai akwai ƙasar sannan za a zauna lafiya, sannan ne mutum zai iya cimma ko wane irin burin da yake da shi.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...