Shin da gaske Coca-Cola da Pepsi mallakin Isra’ila ne? Nasiha zuwa ga masu sharhi

Daga Ibraheem A. El-Caleel

Don Allah almajirai da malamai masu wa’azi suke bincike a kan al’amura kafin hawa mimbari su yi sharhi. Ban san a ina aka samo wannan maganar cewar Coca-Cola da Pepsi kamfanonin ƙasar Isra’ila ne ba.

Google ya fi Facebook amfani. Mu sabawa kanmu da ɗabi’ar bincika abubuwa kafin yaɗa wa jama’a.

A yau da kake karanta rubutun nan:

1. Shekarun Coca-Cola 137 a duniya. An kafa kamfanin tun watan May, 1886.

2. Shekarun Pepsi-Cola kuma 130 a duniya. An kafa kamfanin tun shekarar 1893.

3. Ƙasar Isra’ila kuwa shekarunta 75 kacal ne a duniya. An kafa ƙasar ne a watan May, 1948.

Ka ga kenan Pepsi da Coca-Cola kowannen su ya girmi Ƙasar Isra’ila da fiye da shekaru 50. Ma’ana shine: sai da aka shekara 50 ana shan Pepsi da Coca-Cola a duniya sannan Yahudawan Zionism suka kafa ƙasar Isra’ila.

Don haka Pepsi da Coca-Cola ba mallakin ƙasar Israel bane. Su biyun duka kamfanonin Amurka (USA) ne. Kuma ba mallakin gwamnatin Amurka bane. Waɗanda suka kafa waɗannan kamfanoni mutane ne masu zaman kansu. Kuma a iya binciken da nayi, duk su biyun babu bayahude. Dukkan su biyu Kiristoci ne.

Sannan abinda mutane basu gane ba shine: Coca-Cola da Pepsi da kake sha yanzu haka a Najeriya, ba daga Amurka ake kawo shi ba fa. A’a. A Legas ake buga shi. Wani lokacin hannun jarin mutanen Najeriya ne ma a ciki. Illa dai suna amfani da lasisi ne daga shalkwatar kamfanonin da ke ƙasashen waje. Ka ringa duba board of directors na kowani kamfani, ƙila za ka fahimci su waye masu hannun jari a cikin kamfanin.

Ya kamata mutanenmu su waye. Idan za ka yi nasiha akan Pepsi da Coca-Cola, to ka yi a babin cewa suna ɗauke da sukari (sugar) mai yawa da ke iya illata mutane. Wannan gaskiya ne. Amma maganar wai ƙasar Isra’ila ne ta mallake su, to wannan riwaya ce daga teburin mai shayi. Tarihi bai san wannan ba.

Duk lokacin da ake faɗan Isra’ila ko kuma wani mujrimi ya yi wa Musulinci ɓatanci, kawai sai mutane su fara abubuwa babu tantancewa. Ƙiris ya rage a ce mutane su dena cin goruba saboda asalin goruba daga Ƙasar France ne.

More from this stream

Recomended