Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya a wurin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake gudanarwa a hedkwatar majalisar dake birnin New York na ƙasar Amurka.

Shettima ya halarci taron a madadin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu wanda ya bayyana cewa ba zai samu halartar taron ba saboda zai mayar da hankali wajen wasu ayyuka da suka sha kansa.

More from this stream

Recomended