Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje da Ta’aziyya Jihar Kaduna

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje da ta’aziyya jihar Kaduna na mutanen da harin jirgin sojoji ya kashe a ƙauyen Tudun Biri dake jihar.

Shettima ya sauka a filin jirgin saman sojan Najeriya dake Kaduna.

A yayin ziyarar mataimakin shugaban kasar yana tare da shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Tajuddeen Abbas da kuma shugaban jam’iyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Uba Sani shi ne ya tarbi mataimakin shugaban ƙasar a filin jirgin.

A ranar Lahadi ne wani jirgin sama marar matuki na rundunar sojan Najeriya ya saki bam kan wasu mutane da suke gudanar da taron Maulidi a ƙauyen Tudun Biri dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kawo yanzu dai mutane sama da 100 ne aka tabbatar da mutuwar su a yayin sama da mutane 60 suka jikkata a harin.

More from this stream

Recomended