Shekara uku kenan da Real ta ci Champions League na 12

Real Madrid
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
—BBC Hausa

Ranar 3 ga watan Yuni ne Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai na Champions League na 12, bayan da ta doke Juventus a filin Cardiff a Wales.

Real Madrid ta kai wasan karshe, bayan da ta doke Athletico Madrid 4-2 gida da waje, ita kuwa Juventus nasara ta yi a kan Monaco da ci 4-1 a kakar ta 2016-17.
A wasan na karshe a Cardiff, Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Cristiano Ronaldo daga baya Mandzukic ya farke wa Juventus.
Bayan da ‘yan wasa suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Real ta ci kwallo uku ta hannun Casemiro da Cristiano Ronaldo da kuma Marco Asensio.
Nasarar da Real ta samu a kan Juventus ya sa ta zama ta farko da ta lashe Champions League biyu a jere a sabon fasali da aka yi wa gasar.
Real ta kara bajinta a kakar 2017-18, bayan da ta doke Liverpool ta kuma ci kofin Champions League na uku a jere na kuma 13 jumulla.
A kakar ta 2016-17, Real Madrid karkashin koci, Zinedine Zidane ta yi nasara a wasannin rukuni da ta buga da Sporting da Borussia Dortmund da kuma Legia Warszawa.
Haka kuma Real ta yi nasara a kan Napoli a wasan zagaye na biyu da doke Bayern Munich a karawar daf da na kusa da karshe, sannan ta fitar da Atlético Madrid a daf da karshe.
‘Yan wasan da suka kara tsakanin Real da Juventus:
Juventus: Buffon, Dani Alves, Bonucci, Barzagli Álex Sandro, Chiellini, Khedira, Pjanic, Dybala Mandzukic, Higuaín.
Wadanda suka yi canji (Marchisio da Cuadrado da kuma Lemina)
Real Madrid: Keylor Navas, Carvajal, Varane, Ramos, Marcelo, Casemiro, Kroos , Isco, Modric, Benzema, Cristiano Ronaldo.
Wadanda suka shiga canji (Morata da Asensio da kuma Bale)
Mintunan da aka ci kwallaye:
0-1 (min. 20): Cristiano Ronaldo.
1-1 (min. 27): Mandzukic.
1-2 (min. 61): Casemiro.
1-3 (min. 64): Cristiano Ronaldo.
1-4 (min. 90): Asensio.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...