Shekara Guda Kenan Wadanda Ibtila’i Ya Fadawa Basu Ga Tallafin Da Aka Tara Musu Ba

VOA Hausa

A jihar Bauchi kimanin shekara guda kenan da aka samu ibtila’in ruwa da gobara a garuruwan Bauchi da Azare da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane uku da kuma raunata wasu mutane da dama.

To sai dai tun wancan lokacin mutanen da ibtila’in ya shafa suke zaman jira da zuba ido domin karbar tallafin da hukumomi da gwamnatoci da kuma mutane suka aika masu, amma shuru kake ji kamar an shuka dusa.

Tallafin da aka bayar domin a baiwa jama’ar da ibtila’in ta shafa, sun hada da Tirelolin kayan abinci da kuma miliyoyin Naira da gwamnatin jihar Gombe ta bayar da kuma Naira Miliyan goma da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bada, sai kuma Naira miliyan hamsin da hukumar albarkatun Man Fetur NNPC ta bayar.

Tsohon gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayar da tallafi kayan abinci da suka hada da tirela guda ta shinkafa da kuma tirela guda ta masara da kuma kudi Naira miliyan goma.

Sai dai wasu da wannan masifa ta shafa sunce ko da kwano guda na hatsi basu gani ba, balle a yi maganar kudi.

Kan wannan batu ne Muryar Amurka ta tuntubi shugaban kwamitin raba kayan, farfesa Garba Aliyu Babaji, wanda ya ce an bayar da kayan ta hannun masu unguwanni domin rabawa.

Tsohon kwamishinan harkokin addini, Alhaji Ado Sarkin Aska, ya ce game da kudaden da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo suka bayar akwai ayar tambaya a kansu.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...