Sheikh Daurawa Ya Sauka Daga Shugabancin Hukumar Hisba

Kwamandan Hukumar  Hisba ta Jihar Kano,Mallam Aminu Ibrahim Daurawa ya sauka daga kan muƙaminsa na shugabancin hukumar.

Daurawa ya sanar da saukar tasa ne cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a  shafinsa na Facebook.

Shehin Malamin ya ce dalilin saukar ta sa nada alaƙa da wasu kalamai da yaji sun fito daga jihar Kano.

A wannan makon da muke ciki  ne gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf ya soki aikin hukumar ta Hisba kan yanayin da suke bi wajen kamen masu aikata laifi a otal otal da kuma wasu wurare.

Daurawa ya ce kalaman da gwamnan yayi sun sanyaya masa gwiwa matuƙa dan haka baya jin zai cigaba da jagorantar hukumar.

A ƙarshe ya bawa gwamnan hakuri idan ya yi masa ba dai-dai.

More from this stream

Recomended