Darurruwan mabiya addinin Islama a kafaffen yanar gizo na cigaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyinsu kan sautin muryar fitaccen malamin nan, Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara, da ya nemi afuwar Musulmi kan kalaman da ake zargin batanci ne ga Annabi Muhammad S.A.W.
Akasarin yan Najeriya da suka tofa albarkacin bakin nasu kan lamarin a kafaffen sada zumunta kamar su Tuwita da Facebook, sun bayyana rashin jin dadinsu game da rashin yin bayani mai gamsarwa da shehin malamin ya yi.
A wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa a kafaffen sadarwa na zamani Muhammad Rabiu Rijiyar Lemu, ya koka kan yadda al’umman musulmi ba ta tashi tsaye wajen kare martabar addini ya na mai cewan idan ba’a tuba ba kadan ne masifun da a ke gani a yau a kan wanda ke yiyuwa nan gaba.
Da maraicen ranar Lahadi ne aka fara yada sautin muryar Sheik Abduljabbar, wanda dan asalin jihar Kano ne, ya na neman gafarar Ubangijinsa da al’umman musulmi, kan kalaman na sa ya na mai cewa, wadanda ke sauraron karatuttukan sa kai tsaye sun fahimci yadda abin yake.
Malamin ya kuma ce, wadanda suka fahimci cewa shi ne ya kirkiri kalaman batanci ga annabi Muhammadu S.A.W da ake zarginsa da yi, sun yi wa kalaman nasa gurguwar fahimta ne.
“Wadannan maganganu idan daga ni ne, to duk duniya yau ta ji, ina gaggauta janye su da tuba akan su” malamin ya fada a cikin sanarwar.
To sai dai duk da haka malamin ya dage akan cewa akasarin maganganun da ya fada suna cikin litattafai ne ba shi ba ne ya kirkire su, dalili ke nan da ya ta’allaka tubar ta shi bisa sharadin idan har shi ne ya kirkiro su.
“Idan wannan maganganu miyagun daga ni suke, kirkirar su na yi babu su a litattafan hadisi, ai ko lalle wannan ya isa babban laifi da zunibi da ya wajaba in gaggauta tuba, ba ma sai wani wani ya tilasta ni ba. Wanda kuma ya tilasta ni kan wannan in har daga ni ne, to kuwa ban da masoyi irin sa” in ji Abduljabbar.
Lamarin neman afuwar da Shehin malamin ya yi dai na zuwa ne bayan sa’o’i 24 da fafatawa a wata mukabala tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru da wasu shehunan malamai a Jihar Kano, da gwamnatin jihar ta shirya ta kuma jagoranta.
Daga karshe dai malamin ya yi kira ga al’umman musulmi da su hada kai su kuma mike tsaye domin tabbatar da cewa ba a rusa addininsu na musulunci ba.
A wani bangare kuma, wani dan Sheik Abduljabbar Nasiru ya nemi afuwan al’umman musulmi a kafar Facebook bayan rashin gamsuwa da bayanin da mahaifinsa ya yi game da zargin da aka yi masa na batanci ga fiyayyen hallita.
Idan ana iya tunawa dai, a ranar Asabar da ta gabata ce gwamnatin jihar Kano ta shirya mukabala tsakanin malamin da wasu shehunan malamai daga bangarorin akida daban-daban inda suka tafka muhawar kan kalaman na Sheik Abduljabbar.
Daga karshen mukabalar dai, alkalin da ya jagoranci muhawarar, Farfesa Salisu Shehu, ya yanke hukuncin cewa, malam Abduljabbar ya gaza amsa dukkan tambayoyin da aka yi masa inda daga bisani gwamnatin Kano ta fara shirin gurfanar da malamin a gaban kuliya, kan zargin kalaman batanci da kuma na tunzura al’umma.
(VOA Hausa)