Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana rashin jin dadinsa kan ikirarin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu cewa ba zai binciki yadda aka kashe kudaden tsaro a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.
Sani ya yi wannan furuci ne a cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Talata.
A cewarsa, matakin Shugaban Kasa na kin binciken kudaden tsaro ya saba wa kokarin da gwamnati ke yi na binciken harkokin Babban Bankin Najeriya (CBN), karkashin tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele.
“Idan ka samu wannan matsayi a kasa mai matsaloli irin namu, wajibi ne a binciki inda kudaden jama’a suka tafi, kamar yadda ake yi a CBN,” inji Sani.
Ya kara da cewa, “Amma lokacin da aka tambayi Shugaba Tinubu kan satar kudaden tsaro a karkashin gwamnatin Buhari, sai ya ce yana duba gaba, ba baya. Wannan matakin ya saba wa yadda aka koma baya aka binciki CBN.”
Sanatan ya zargi matakin Shugaban Kasar da zama tamkar lada ga masu satar kudaden jama’a. “Idan ka ce abin da ya faru ya wuce, hakan na nufin ka goyi bayan cin hanci da rashawa,” inji shi.