
Shanu kusan 18 ne suka mutu bayan da ake zargin sun yi kiwo a wata gona da aka yiwa feshin magani a garin Vwei dake karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.
A cewar wasu majiyoyi dake garin lamarin ya faru ne wajen karfe 12:00 na ranar Laraba lokacin da shanun mallakin wani mai suna Danazumi Haruna suka yi ratse cikin gonar da aka yiwa feshin magani.
Bakwai daga cikin shanun an samu damar yanka su nan take a yayin da 11 suka mutu nan take.
Karin wasu shanu 17 da abun ya shafa na can na samun kulawar jami’an kula da lafiyar da dabbobi.