Sevilla: Sarakan gasar Europa League sun sake lashe ta a karo na shida

Sevilla

Bayanan hoto,
Babu ƙungiyar da ta lashe gasar sau huɗu sai Sevilla mai guda shida

Sarakan Gasar Europa League – Sevilla – sun sake lashe gasar a karo na shida bayan sun lallasa Inter Milan da ci 3-2 a birnin Cologne na Jamus a daren Juma’a.

Sevilla ta sake kafa tarihin lashe kofin fiye da kowacce ƙungiya a Turai, inda Inter Milan ke biye mata da guda uku.

Wasa ya ɗauki ɗumi ne bayan ɗan wasan bayan Sevilla Diego Carlos ya doke Romelu Lukaku, abin da ya jawo bugun finareti, sannan wasan ya ƙare bayan Lukaku ya ci gida sakamakon watsiyar da Carlos ya yi.

Hakan na nufin Inter Milan za ta ci gaba da jiran lashe kofin Nahiyar Turai na tsawon aƙalla shekara 10 – tun bayan Champions League da ta lashe ƙarƙashin Jose Mourinho a 2010.

Finaretin da Lukaku ya ci ne ya fara buɗe wasan da ƙwallonsa ta 34 a dukkanin wasannin kakar bana kuma ta 11 a Europa na bana.

Luuk de Jong ne ya farke kuma ya ƙara dukaninsu da ka kafin Lukaku ya ci gidaa minti na 74.

More from this stream

Recomended