Saudiya za ta taimakawa CBN da kuɗaɗen kasashen waje

Ƙasar Saudiya ta yi alkawarin samar da isassun kuɗaɗen kasar waje ga Najeriya domin taimakawa shirin Babban Bankin Najeriya(CBN) na kawo sauye kan yadda ake musayar kuɗaɗen waje.

Kasar ta Saudiyya dake da matukar arzikin man fetur ta kuma yi alkawarin zuba jari wajen farfaɗo da matatun man fetur na Najeriya.

Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman shi ne ya yi wannan alkawarin a wata ganawa da suka yi da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a wurin taron kasashen Afrika da na Larabawa dake gudana a birnin Riyadh.

Jawabin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a,Muhammad Idris Malagi ya fitar.

Yariman ya yabawa sauye-sauyen tattalin arziki da Tinubu yake aiwatarwa inda ya tabbatar da goyon bayan kasarsa wajen cimma nasarar sauye-sauyen.

More from this stream

Recomended