Saudi Arabia na maraba da masu aikin Umrah

Hajj

Saudiyya ta sanar da za ta kyale mazauna ƙasar su gudanar da ayyukan ibada na Umrah bayan ta dakatar da komai na tsawon watanni.

Hukumomin ƙasar sun ce daga baya za su kyale maniyyata dag ƙasashen waje su shiga ƙasar domin gudanar da ibadar wadda ta ke da muhimmanci ga Musulmin duniya, sai dai za ta ƙayyade yawan maniyyatan da yawan ƙasashen da za ta bari su shiga ƙasar.

Maniyatta da ke cikin Saudiyya na iya yin Umrah daga ranar 4 ga watan Oktoba, inda maniyattan da ke ƙasashen ƙetare kuwa sai sun jira zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba kafin su sami izinin shiga ƙasar.

Ma’aikatar Aikin Hajji ta Saudiyya ta kuma bayyana cewa idan annobar korona ta gushe, za ta kyale dubban maniyatta daga ko’ina a duniya su ci gaba da ziyartar biranen Makkah da Madin domin gudanar da ibadunsu.

Musulmi na iya yin ibadar Umrah a duk lokacin da suka so, ba kamar aikin Hajji ba da ake iya yi sau É—aya kawai a kowace shekara.

Miliyoyin Musulmi daga sassan duniya kan tafi Saudiyya a kowace shekara domin sauke wannan muhimmiyar ibada da ke ta biyu ga aikin na Hajji a daraja.

Tun dai a watan Yulin bana hukumomin Saudiyya suka ɗauki matakai domin daƙile bazuwar annobar korona, A bana mutum 10,00 ne kawai suka yi aikin Hajji a maimakon kimanin miliyan biyu.

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...