Sau uku ina tsallake rijiya da baya a harkar fim, inji Kamaye

Kamaye

Hakkin mallakar hoto
Kamaye

Image caption

Dan Azumi BAba kan fito a matsayin Kamaye kuma talaka futuk a fim din Dadin Kowa

—BBC Hausa

Fitaccen mai fitowa a fina-finan Hausa a Najeriya, wanda kuma yake bayar da umarni Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa ya ce sau uku yana tsallake siradin mutuwa a tsawon shekarun da ya shafe yana harkar fina-finai.

Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye saboda fitowar da yake yi a shirin Dadin Kowa na tahsar talbijin ta Arewa24, ya shaida wa BBC hakan ne a wata hira ta musamman da ta yi da shi ta waya.

Ya ce: ”Akwai abubuwa da suka faru da ni a tsawon lokacin da na yi ina wannan harka da ba zan manta da su ba tun da da kyar na tsallake rijiya da baya ban hallaka ba.”

Gamuwarmu da gwamna

Lamari na farko da Kamaye ya ce ya kusa zama ajalinsa shi ne wata rana suna daukar fim din Bakandamiyar Rikicin Duniya a gadar nan da ta yi hanyar Kura a wajen garin Kano,

”Sai muka je daukar wata fitowa da ake sace boss din fim din inda za a kwace shi a hannun jami’ai. To a lokacin ba mu san yadda lamarin yake ba sai muka hau haka tsakiyar kwalta da nufin a nan za a yi daukar.

”To a lokacin wani gwamna ne na soja yake mukli, mun fara hakar tsakiyar kwalta ba mu yi nisa ba sai muka ji jiniyar tahowar gwamna. Sai muka tarwatse a guje muka shiga karkashin gadar muka buya.

”Ashe tuni securiy sun gano mu. Muna kwance karkashin gada sai ji muka yi duk an ritsa mu da bindiga, aka fito da mu.

”Sai suka tambayi abin da muka zo yi. Sai muka ce fim muke shiryawa da kuma nufinmu. Sai suka gane rashin sani ne ya sa muka zo yin wannan abun. Kuma abin da ya ceci mu ma daya daga cikinmu Aminu Hassan Yakasai yana cikin kungiyar ‘yan jarida ta NUJ ya nuna katin shaidarsa.

”To da kansa gwamnan a lokacin ya fito ya ce ba haka ake yi ba, kamata ya yi mu nemi ilimin abin. To daga baya gwamna ya ce lallai mu je mu nemi kwarewa kuma ya yi alkawarin ba mu gduunmowa don ci gabanmu.

”To ka ga a lokacin da a ce irin yanzu ne da duniya ta gurbace da masu satar mutane da fashi da makami lallai ba abin da zai hana jami’an tsaron nan bude mana wuta tun daga nesa.

Tudun Wada

Darakta Dan Azumi ya ce lamari na biyu da ya kusa zama ajalinsa shi ne wata rana da ya je karamar hukumar Tudun Kano ta jihar Kano da nufin nuna wani fim dinsa a sinima.

“To kamar da hantsi haka sai na tafi yawo bayan gari. Ina tafiya sai na hango wasu duwatsu sai na ga za su yi kyau a yi fim a wajen, kawia sai na ci gaba da durfafarsu don na gano yadda wajen yake sosai.

”Har na yi nisa sosai sai na ji wani BAfulatani yana kwalla min kira yana ‘hoi,hoi’. Sai na tsaya tun da na ga alamar da ni yake. Sai ya isko ni ya ce Bawan Allah ina za ka je a nan wajen? Sai na ce ina duba duwatsun nan ne saboda ina so wata rana na zo na yi fim a wajen.

”Sai ya ce min to ai Allah Ya kiyaye ka, ka ga wancan dutsen da kake durfafa, to a nan wajen akwai wata katuwar mesa da ta taba hadiye min dan marakina (dan saniya). Don haka ba a zuwa don akwai manya-manyan macizai da mesa masu hadiyae mutum. Ta hadiye dan saniya ma balle mutum.”

Kamaye ya ce a take jikinsa ya hau tsima tare da yi wa Bafulatani godiya, sai ya kama hanya ya juya inda ya fito.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Daga Bakin mai ita tare da Dan azumi Baba

Gashuwa

Karo na uku da daraktan ya tsallake rijiya da baya kuwa a garin Gahuwa ne na jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, inda can ma ya je nuna fim ne a sinima.

A wata safiya sai ya shiga cikin gari har zuwa bayan gari don dubo ko akwai wani waje da zai yi kyau da daukar fim da ba kowa ne ya taba yin aiki a wajen ba.

”Ina kewayawa sai na ga wani waje yashi ne fululu ya yi kamar na Hamadar Sahara gado-gado din nan, sannan ya yi kama da yashin kankara wato snow. Har na tunkari wajen gaba-gadi sai na ji wani yana kwalla min kira.

”Allah Ya so ban yi girman kai ba sai na tsaya don saura kiris na karasa wajen. Sai ya ce min Malam hala kai bako ne, sai na ce e. Ya ce me ya kawo ka nan wajen? Na ce na zo haska fim ne daga Kano, shi ne na zo ina neman wajen da zai yi kyau da daukar fim nan gaba idan zan yi.

”Sai ya ce to Allah Ya kiyaye ka, wannan wajen yana da kyau amma fa yana da ban mamaki, tsaya ka gani. Sai ya dauko dutse ya wurgo a cikin yashin daga farko-farkonsa.

”To ashe ba yashi ba ne, don kuwa yana jefa dutsen sai wuta ta taso daga ciki, shi kuma dutse y lume. Sai ya ce min to ka ga wannan wajen rami ne, shekara da shekaru a nan ake shikar shinkafa ko alkama. To ana haka ana haka da yake trana ta gama dukan buntun shinkafar sai ya kma da wuta.

”Dama ka’idar buntu idan ya kama da wuta za ka ganshi ya yi fari tas gwanin sha’awa. Sai ya ce to nan wajen shikar shinkafa ne ya yi gobra, kum rana ce ta kona shi ba wai wuta aka sa masa ba.

”Sai mutumin ya ci gaba da cewa to tsakanin mutune da dabbobi, Allah kadai Ya san yawan wadanda suka kone suka mutu a ciki. Allah ya kiyaye ni da ni ma na zama tarihi.

Kamaye ya ci gaba da cewa wannan lamari ya matukar firgit shi ba kadan ba. Ya ce mutumin ya gaya masa cewa an yi damina da dama amma ruwanta bai kashe wutar wannan waje ba.

”Sai na cewa mutumin to ba a taba kiran ‘yan kwana-kwana ba? Sai ya ce abin da ruwan dmaina bai kashe ba yaya za a yi ‘yan kwana-kwana su iya kashewa. ”

Dan Azumi Baba ya ce saboda al’ajabi bai hakura ba sai da ya bari bayan tsawon lokaci ya sake komawa garin don ganin halin da ake ciki. ”To sai na je wajen na tarar da mutane sun kewaye ramin suna karaun Al-Kura’ni wasu kuma suna ta alkunutu.

”Sannan daga gefe kuma an haka burtsatse ana debo ruwan ciki ana zuba tokar buntun ‘yar kadan ana zuba mata ruwa kamar jarka daya sannan take mutuwa, sai tokar ta koma baka alamar wutar ta mutu.

”To iya zaman a garin na kwanaki kullum sai sun yi wannan aikin,” in ji Dan Azumi Baba.

A don haka ya ce wadannan abubuwa ne da ba zai taba mantawa da su ba a rayuwarsa.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...